DANDALIN YADA ILIMIN AHLUL-BAYT
DANDALIN YADA ILIMIN AHLUL-BAYT

DANDALIN YADA ILIMIN AHLUL-BAYT

PLURALISM A ADDINI


GABATARWA


Na zavi in yi rubutu a kan wannan aqida ta Puluralizim ne saboda qarancin saninta da muke da shi musamman ma a qasarmu mai albarka Nigeria.

Domin yin bincike da rubutu a kan irin wadannan aqidu da a qasashenmu ba`a sansu ba sosai a suna sai dai a aikace yana da matutaqar mahimmancin gaske.

Yin rubutu a kan irin wadanann aqidu zai sanya mutanenmu su fahimci haqiqanin aqidun da manufarsu da illarsu.

Lokacin da aka san abu sai a iya sannin yadda za`a yi mu`amala da shi, da yadda za`a kauce ma matsalolinsa da aibobinsa.

Don haka ne ya zama dole mu bada himma domin bincike a kan irin wadannan aqidu da kuma bayyanar da su ga mutane ta hanyar rubutu da magana.

.Dafatan Allah ya sa mu dace.



"MA'ANAR "PLURALISM


"Ita wannan Kalmar ta “Puluralizim” kalmace murakkaba (da ta hauhawa), a harshen Engilish daga "pulural" da "ism.

Za'a iya tarjamata da ma'anar "karkata ga yawa" ko "Yawaitar hanya ko addini".[1] pluralism tana nufin yadda da yawa da kore takaitawa a vangarori mabanbanta, kamar palsapa, siyasa, wayewa, alumma, addini...

.

Amma mu anan zamu taqaita ne kan magana kan  pluralism (karkata ga yawaitar addini).


Amma  pluralism ya kasu zuwa gida biyu:

1-Ta wajen addini: wato aqidar karkata ga yawaitar addinai.


2-Ta cikin addini: wato aqidar karkata ga yawaitar mazhabobi a cikin addini daya.

Dukkan addinai ko wasu adadi na addinai a zamani daya suna tare da gaskiya da kuma samun kubuta.

Dan haka addinin Musulunci yana a kan gaskiya haka ma Yahudanci da Masihanci[kiristanci] suna a kan gaskiya, hakama sauran addinai, mabiya addinai mabanbanta zasu iya rayuwa ba tare da wani rikici ba...


Amma farkon al'amari Puluralizim a bangaran Kilisa tana nufin mutumin da ke da matsayi da aiki mai yawa kuma mabanbanta.

PLURALISM DIN tazo a littafin Lutaseh mai suna “Ma ba'adattabi'a” a shekara ta 1841 miladi, wanda ya zama shi ne karo na farko da ta shiga Palsapa[2].

 pluralism Dinyana nufin ma'aika da hanya ta tunani wanda take da aqidar cewa dukkan addinai ko wasu adadi na addinan da suke a zamani guda suna kan gaskiya da kuma samun tsira,  kuma basu yadda da a taqaita addini da aqida ko taqaita tsira da gaskiya a addini daya ko mazhaba xaya ba. Basu yadda da taqaita bin addini ko shari'a daya ba.

Suna cewa: "haqiqa muxlaq" ce (haqiqa sake ba qaidi ce), "haq muxlaq" ce (gaskiya sake ba qaidi ce), wato akwai gaskiya a cikin kowane addini[3]. Jan hik yana cewa: ...tambayoyin masihi (Kirista) suna qarewa ne da cewa: ta yaya mutun zai zamo mai gaskiya? 

Ko wane daya daga cikin manyan addinai na duniya, amsa ce ga gayar haqiqa (ko wane dai dai ne), koma ko wane daya daga cikinsu yana samar da hanyar tsirar mutun[4].

Na samo daga littafin puluralizim dini az manzare Qur'ane karim.na Aliyu Islamin, s: 27-29.





zamu ci gaba............



[1] -farhange kamil engilizi farsi, j: 4, 4091, farhange jami'i fidhru aryanfur, j: 4, s: 3949. Farhange fushirde -engilizi, engilizi, engilizi-parsi, s: 921. Naqaltowa daga Puluralizim Dini az manzare Qur`an, S: 27.

[2] -nak: nameh farhang, 24, s: 4.

[3] -nak, mabahese puluralizim dini, s: 177-165, 78-73, 69, 65.

[4] -palsape din, s: 300, bi naqal az kitabe kalame masihi, jan hik, s: 41. Naqaltowa daga Puluralizim Dini az manzare Qur`an, S: 27-29.

نظرات 0 + ارسال نظر
امکان ثبت نظر جدید برای این مطلب وجود ندارد.