DANDALIN YADA ILIMIN AHLUL-BAYT
DANDALIN YADA ILIMIN AHLUL-BAYT

DANDALIN YADA ILIMIN AHLUL-BAYT

KOGI DA YAFI NONO FARI YAFI ZUMA ZAKI

                                                   


Hakika watan Rajab da sha'aban da Ramadan watanni ne masu kololuwar daraja da falala.


Manzon Allah (s.a.a.w) yace:- "Hakika Rajab watan Allah madaukaki ne babu wani wata da yayi kusa dashi a falala daga cikin watanni masu girma, haramun ne a yaki kafirai a cikin shi. Ku saurara Rajab watan Allah ne, Sha'aban watana ne, Ramadan kuma watan al'ummata ne, wanda duk ya azumci wuni a Rajab yardar Allah mafi girma ta wajaba akan shi, sannan kuma fushin Allah zaiyi nesa dashi sannan kuma za'a rufe mashi kofa daga cikin kofofin wuta".


A wani hadisi Imam khazim(A.S) yana cewa:- Duk Wanda ya azumci wuni daya a Rajab wuta zatayi nesa dashi gwargwadon tafiyar shekara daya, wanda ya azumci wuni uku aljannah ta wajaba a gareshi. Ya kuma kara cewa Rajab wani kogi ne a cikin aljannah da yafi nono fari ya kuma fi Zuma zaki, wanda duk ya azumci wuni daya a cikin shi Allah zai shayar dashi daga wannan kogin.


Imam sadiq (A.S) yace a cikin wani hadisi:-Ma'aiki yace Rajab watan istigfari ne ga al'ummata ku yawaita istigfari a cikin shi domin Allah mai rahma ne da jinkai, an kirashi da Rajabul Asabbu saboda rahma tana sauka sosai ga al'ummata a cikin shi ku yawaita fadin

نظرات 0 + ارسال نظر
امکان ثبت نظر جدید برای این مطلب وجود ندارد.