DANDALIN YADA ILIMIN AHLUL-BAYT
DANDALIN YADA ILIMIN AHLUL-BAYT

DANDALIN YADA ILIMIN AHLUL-BAYT

(TAKAITACCEN TARIHIN IMAMI NA BIYAR (5) ACIKIN JERIN IMAMAN AHLIL BAITI (Imam Bakir) (AS

بسم الله الرحمن الرحیم


Sunanan shi Muhammad dan Imam Ali Zainul Abideen dan Imam Hussaini dan uwan Imam Hassan dan Imam Ali dan Abi Dalib mijin Sayyaidah Fatima Yar Annabi Muhammad (S.A.A.W).


Sunan mahaifiyar Imam Fatima Yar Imam Hassan shugaban Samarin Aljannah ana yi mata alkunya da ummu Abdillah. 


Sanya sunan Imam 


Manzon Allah (S.A.A.W) ne ya sanya mishi suna tun kafin a haife shi da shekaru gomomi, haihuwar Imam tana daga cikin labaran gaibi da Allah ya gayama Manzon Allah (S.A.A.W).


 Wata rana Manzon Allah (S.A.AW) yana cikn Sahabban shi sai Imam Hussaini (AS) ya shigo,  sai Manzon Allah (S.A.A.W) ya nuna Hussain (AS) yace, za'a haifama wannan dan nawa, wani da anace mashi Ali bin Hussaini shugaban masu ibadah (Zainul abideen).


Manzo ya cigaba da cewa wata ranar Juma'a kuma za tazo sai wani mutum yazo yayi kira ya cema Imam Zainul abideen tashi! Sai Imam ya mike, sai mutumin yayi mashi bushara da za'a haifa mashi da sunan shi Muhammad za'ayi mashi lakabi da Bakir.


Sai Manzo ya juya ya kalli sahabin shi Jabir bin Abdullahi Al-ansari yace mashi "za kayi tsawon rai har lokacin da za'a haife shi idan ka riske shi kace ina gaishe shi.

Ka sani ya Jabir Mahdi daga cikin yayan shi zai fito, ka Sani ya Jabir bayan nan ba zaka dade ba zaka koma ga Uban gijinka". 


Kuma lallai abinda ya faru kenan Jabir ya wanzu yana jiran haihuwar Imam ya Isar da sakon Manzo (S.A.A.W), sai wata rana yana zaune a gidan shi a Madina Imam Zainul abideen ya ziyarce shi tare da dansa Imam Bakir sai Jabir yace wanene wannan? Sai yace mashi dana ne Muhammad sai Jabir yayi kuka yace ya Muhammad Manzon Allah yana gaisheka.  Malaman tarihi wasu sun tafi akan cewa a wannan daren Jabir yayi wafati wasu kuma sunce bayan nan da watanni wasu kuma sunce bayan nan da shekara 2, wasu 3.


Al-kunyar Imam da Lakubban sa


Anayi mashi al-kunya da Abu Ja'afar 


Lakubban shi kuma 1. Ameen 2.Shakeer 3.Hadi 4.Sabeer Shaheed 5.Bakir wannan shine mafi shaharar lakabin shi 


Tarihin Haihuwar shi


An haifi Imam Bakir ranar juma'a cikin watan Rajab shekara ta 56 ko 57 ko kuma 58 bayan hijira.

Wato wasu malaman tarihi sun tafi akan kafin waki'ar Karbala da shekara 4,3,2


Haibar Imam da Tsoron Allah: 

Siffar Imam da haibar shi irin ta Annabawa ce, babu wani mutum daya taba zama dashi face yayi mashi haiba (kwar jini), wata rana wani babban Malamin Fiqhu na Basara mai suna Qatada yace ma Ibni Abbas "na ziyarci Imam Bakir wallahi wani mutum bai taba yimin kwar jini a ido da zuciya ba kamar shi".


A bangaren danfaruwar shi da Allah kuwa hatta a jikin zoben hannun shi abinda aka rubuta shine(العزة لله جمیعا) wato dukkan iko da karfi na Allah madaukakin Sarki ne



Inda Imam ya rayu.


Imam da kakan shi Imam Hussaini shekara uku da watanni da mahaifin shi Imam zainul abideen kuma shekara 34 a Madina tsawon rayuwar shi yana bada karatu yana kuma sabunta ilimi har karshen rayuwar shi. Yayi Shahada ne ta hanyar zuba mashi guba da Sarkin banul Abbas mai suna Abdulmalik yayi a ranar litinin 7 ga zulhajj shekara ta 114 bayan hijira.


Sign:- FOSA EDITORIAL COMMITTEE FUNTUA CHAPTER.

 

alhujjah.blogsky.com

نظرات 1 + ارسال نظر
salis سه‌شنبه 14 فروردین 1397 ساعت 20:32

************************

امکان ثبت نظر جدید برای این مطلب وجود ندارد.