HAIHUWA ITACE MUSABBABIN WANZUWAR RAYUWA
Danda mutum ya haifa shine abinda zaisa a rika tunawa da mtutm bayan bashi, a zahirin al’amari danda zamu tafi mu bari shine zai zama gaado na hakika da zamu tafi mu barshi a doron kasa , wanda zai zamo mai bauta ga ubangiji kuma mai nemar ma iyayensa gafara daga gareshi.
Da na gari, zai iya zama dalilinda zaisa iyayensa su zama abin yabo a bayan babu su, ya kuma zama sanadiyyar wanzuwar tunaninsu a zukatan al’umma .
Madalla da iyaye masu barin y’ay’aye irin wadannan da zasu zamo magadan halaye da kuma siffofiN iyayensu na gari .
IMAM RIDHA (A.S) YACE :
“ duka wanda bai bar da a duniya ba , kamar wanda baiyi rayuwa a cikin al’umma bane, amma wanda ya rasu yabar dansa a duniya kamar wanda yake rayuwa da al’umma ne (dukda cewa ya rasu)”[1]